‘Yan Ansaru nata ɗaura aure da ‘yan mata a Jihar Kaduna

0
474

Yan ƙungiyar Ansaru na ɗaura aure tsakanin mayaƙanta da ‘yan matan yankin Birnin-Gwari a Jihar Kaduna.

BBC ta ruwaito cewa irin wannan lamari ya faru ne a garin Tsohuwar Kuyallo, inda wasu ‘ya’yan ƙungiyar suka angwance da ‘yan matan garin a ranar Talata.

Wani mazaunin yankin Birnin Gwari ya tabbatar wa BBC da ɗaurin auren, inda ya ce ba sabon abu ba ne a yankin.

Ya ƙara da cewa ko a watanni kimanin biyu da suka gabata mayaƙan ƙungiyar sun haɗa aure da wasu ‘yan mata biyu a yankin.

BBC ta tuntuɓi rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kaduna game da wannan lamari, inda ta ce tana gudanar da bincike a kai.

Sai dai masana harkokin tsaro kamar Muhammad Kabir Isa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, na ganin sakacin gwamnatin Nijeriya ne ta fuskar tsaron ya sa ƙungiyar ke amfani da irin waɗannan hanyoyi domin samun shiga tsakanin al’umma, har abin ya kai ga haɗa zuri’a.

“Yanzu idan suka yi aure cikin jama’a, yaran gidan ko mazan da ke ciki sun zama nasu, waɗannan duk dabaru ne na samun mabiya da mutanen da za su dauki akida da ra’ayoyinsu,” in ji Muhammad Kabir.

Ya bayyana cewa kulawar da gwamnati ta gaza bayarwa ne har ya sa ƙungiyoyi kamar Ansaru ke shiga cikin al’ummomi domin ba su tallafi domin jawo ra’ayinsu.

Yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna na daga cikin yankunan da ƙungiyoyin tayar ƙayar baya suka addaba.

Yanki ne da a tsawon shekaru ‘yan fashin daji ke kai hare-hare a garuruwa da kuma kan matafiya a hanyoyi, inda suke kashewa ko garkuwa da su.

Sai dai a baya-bayan nan yankin ya ƙara shiga tasku, bayan da rahotanni ke ta nuna cewa ƙungiyar ta Ansaru ta samu gindin zama a nan.

An riƙa samun bayanai kan yadda suke iko da wasu yankunan na Birnin Gwari, har ta kai ga suke da wuƙa da nama kan abubuwan da ke faruwa a wasu garuruwan.

Kamar yadda binciken cibiyar Nazari kan tsaro ta ISS ya nuna, Ansaru ta kafu ne a wasu yankunan Arewacin Nijeriya shekaru 10 da suka wuce.

Kuma ta samu ne bayan ballewar wasu ‘ya’yan babbar ƙungiyar Boko Haram, a dalilin rashin jituwa tsakanin masu matsakaici da kuma masu tsattsauran ra’ayi.

Kuma tun daga lokacin take faɗaɗa hanyar ƙulla ƙawance da ƙungiyoyin ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a yankin.

Leave a Reply