Yalon kati ya hana Slovenia hawa mataki na biyu a guruf ɗin gasar Euro 2024

0
52
Yalon kati ya hana Slovenia hawa mataki na biyu a guruf ɗin gasar Euro 2024

Yalon kati ya hana Slovenia hawa mataki na biyu a guruf ɗin gasar Euro 2024

Yayin da ake kammala zagayen matakin guruf-guruf a gasar Euro 2024 da ke gudana a ƙasar Jamus, a Rukunin C, ƙasashen Slovenia da Denmark sun yi kankankan a yawan maki da yawan ƙwallaye, inda duka suka ƙare da maki uku.

A rukunin nasu, Ingila ce ta zo ta farko da maki 5 bayan ta ci wasa ɗaya kuma ta yi canjaras sau biyu. Sai Serbia da ta zo ta ƙarshe da maki biyu, bayan ta yi canjaras sau biyu da rashin nasara sau ɗaya.

Sai dai ba a iya tantance wace ƙasa ce ta biyu ba a rukunin, kasancewar Denmark da Slovenia kowannensu yana da maki uku, bayan yin canjaras sau uku. Ko da aka duba yawan ƙwallayen da kowa ya ci da waɗanda aka ci shi, ƙasashen sun kuma yin arba.

Wannan ne ya tilasta wa hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA yin amfani da wata dokar da ba a saba jin ta ba, don fayyace waye yake mataki na biyu, don a san da wa zai kara a matakin gaba na ‘yan-16.

KU KUMA KARANTA: Manchester City ta lashe Firimiyar Ingila sau huɗu a jere

Sakamakon haka ne, aka duba wace tawaga ce ta fi ladabi, inda aka duba yawan katin gargaɗi da aka bai wa kowace ƙasa cikin wasanni uku da suka buga. Sai dai an kuma samun yawan katin nasu shi ma daidai ne.

A nan ne UEFA ta duba cewa cikin yalon katunan da aka bai wa tawagar Slovenia, akwai ɗaya da aka bai wa mataimakin kocinsu, Novakovic Milivoje, wanda ya sa aka yanke hukuncin cewa hakan ya nuna Denmark sun fi Slovenia nuna ladabi.

Wannan ne ya ba wa ƙasar Denmark dama ta samu haye wa gaban Slovenia inda ta zamo a mataki na biyu a rukunin, kuma ta tsallaka zuwa matakin siri-ɗaya-ƙwale kai-tsaye.

Amma kuma duk da cewa Slovenia ta ƙare a mataki na uku, ta samu cancantar wucewa matakin na gaba, wanda shi ne karon farko da ta kai irin wannan mataki a wata babbar gasa, a tarihin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here