Yadda wani mutum yayi wa Yaro fyaɗe har ya mutu

2
540

Rundunar ‘yan sanda ta kama wani ɗan luwadi mai  shekaru 36 mai suna Sikiru Ajibola da ake zargi da ya yi wa yaro ɗan shekara biyar fyade kuma ya mutu, lamarin da ya faru  a yankin Ogijo da ke jihar Ogun.

 Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar sun kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a bayan wani rahoton da shugaban kungiyar ci gaban al’umma (CDA) na Olorunwa Arogbeja Ogijo ya gabatar a ofishin ‘yan sanda na  Ogijo. 

A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi,  wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya shaida cewa yana cikin yin lalata da yaron, sai ya mutu, inda ya haƙa rami ya binne gawar yaron.

“Ya kuma kai ‘yan sanda inda inda ya  binne gawar” inji shi.

 Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, CP Lanre Bankole ya bayar da umarnin miƙa wanda ake zargin  sashin binciken kisan kai na jihar domin ci gaba da bincike kafin daga bisani a kai shi kotu.

2 COMMENTS

Leave a Reply