Yadda uba ya kori ɗansa don ya ziyarci mahaifiyarsa

0
519

Wata mace da ke zaune a ƙaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna, Hindatu Haruna ta ce tsohon mijinta ya kori ɗanta ne saboda yawan ziyarar da ya ke kai mata.

Hakan na ƙunshe ne a wani rubutu da wata ‘yar gwagwarmaya a shafukan sada zumunta, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a Facebook, inda tace Aliyu Nuhu wanda aka kora yaro ne ɗan shekara 17.

A zantawarta da ‘yan jarida ta wayar tarho, mahaifiyar cikin ruɗani ta bayyana cewa mahaifinsa ya kore shi ne bayan ya samu labarin cewa yana zuwa gidanta.

KU KALLI BIDIYON ANAN: https://youtu.be/B_lYSZ5RcBw

“Na ji cewa bayan Aliyu ya dawo gida, mahaifinsa ya tambaye shi daga ina yake? Aliyu yace ya ziyarceni, sai mahaifinsa ya fusata ya ce ya tattara kayansa ya koma gurina.

Aliyu ya san ni na auri wani kuma ba zai iya zuwa ya zauna da ni ba,” in ji ta.

KU KUMA KARANTA:Yadda mace ta yanke azzakarin mijinta, ta kashe shi har lahira

Ta kuma ce ɗanta ya bar gida a watan Disamban 2022 amma babu wanda ya sanar da ita.

Ta ƙara da cewa ” Sai makon da ya gabata na sami labarin, kuma tun lokacin ban yi barci ba.”

Ta yi kira ga jama’a da su taimaka mata wajen neman ɗanta da ya ɓace, inda ta ce duk wanda ya san inda yake to ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma wajen wani basaraken gargajiya a Zariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here