Yadda tsohon Kwamishina ya kashe abokinsa kan ‘Yarsa da yake nema

0
400

Ana zargin Basarake kana tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Bauchi Mohammed Galadima Damina da kisan abokinsa, kana maƙwabcinsa mai suna Adamu Babanta, wanda yake zargin tsohon Kwamishinan da yunƙurin yin lalata da ‘yarsa.

Lamarin ya faru ne a unguwar Yelwan Lebra, da ke wajen birnin Bauchi da yammacin Lahadi, 30 ga Oktoba, 2022.

Rahotanni sun nuna cewa Marigayin , mai shekaru 68, wanda tsohon ma’aikacin gwamnatine ya kama amininsa tare da ‘yarsa a yammacin ranar Lahadi, yana ƙoƙarin yaudararta domin yayi lalata da ita, lamarin da ya ɓata masa rai ya kuma yi yunƙurin ɗaukar mataki amma abokin nasa ya buge shi da mota, lamarin da yayi ajalinsa.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, tsohon Kwamishinan ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan yada labarai da kuma Kwamishinan ayyuka na musamman a lokacin mulkin tsohon gwamna Isa Yuguda a karo na biyu. Kana yana riƙe da sarautar gargajiya ta Galadiman Dass a masarautar Dass ta jihar Bauchi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun shawo kan matasan da suka fito zanga-zanga bayan kashe wani mai shekara 67

Mazauna yankin sun shaida cewa wanda ake zargin ya kira ‘yar abokinsa ta waya domin tazo su haɗu da shi a wani gidan mai.

A cewar wani ɗan uwan mamacin da bai so a bayyana sunansa ba, Galadiman na Dass da marigayin abokai ne kuma makwabta ne.

“Ana zargin cewa Galadima ya yi yunƙurin yin lalata da ‘yar amininsa mai shekaru 18, mai suna Khadija, bayan yayi ta bibiyarta da ta zo su haɗu, inda yayi ta tura mata katin waya.

“Hakan ne ya sanya Khadija ta shaida wa mahaifiyarta, wacce ta shaida wa mahaifin yarinyar cewa abokinsa na neman ‘yarsa da lalata, amma yaƙi yarda da maganar sai a ranar Lahadin da tsohon Kwamishinan ya kira Khadija ya kuma nemi ta same shi a Unguwar Yelwan Lebura, sai mahaifin nata ya nemi ta fita zai biyo bayanta ya tabbatar.

Ko da ta tafi ta tarar da tsohon Kwamishinan, inda ya buɗe mata mota ta shiga, hakan ne yasa Marigayin ya doshi motar abokinsa a fusace ko da tsohon Kwamishinan ya gan shi sai yayi yunqurin barin wajen da motar, yayin da Marigayin ya cusa hannunsa cikin motar yana ƙoƙarin kashe injin motar, nan take tsohon Kwamishinan ya buge kan abokinsa a jikin garun da ke gefe, ya kuma take kafafunsa da motar lamarin da yayi sanadiyar mutuwarsa bayan an yi ƙoƙarin ceton rayuwarsa a asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa” inji shi.

Al’ummar ‘yankin sun gudanar da zanga zanga a ranar Litinin inda suka tushe hanyoyi suka hana zirga zigar ababan hawa har sai da jami’an tsaron da suka haɗarda soji da ‘yan sanda suka kwantar da tarzomar da ta biyo bayan zanga zangar.

Hukumar ‘yan sanda a jihar ta Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, a cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi Ahmed Wakili, rundunar ‘yan sandan na bincike game da lamarin.

Leave a Reply