Yadda tsoho ya ƙone agwalansa biyar, bayan ya sanya man fetir a ɗakin kwanansu

0
648

Joseph Ojo, tsoho ne mai shekaru 64, ya bayyana dalilin da ya sa ya ƙona ‘yan agulansa su biyar, yace gaɗuwa suke da matarsa wato uwarsu su lakaɗa masa duka.

Tsohon wanda ‘yan sanda suka kama shi suka kuma gabatar da shi ga ‘yan jarida a hedikwatar ‘yan sandan Najeriya da ke Akure, jihar Ondo, ya bayyana cewa ‘yan agolan nasa ne suke haɗuwa da mahaifiyarsu suyi ta masa duka, kuma bada ba shi abinci duk da shi ne ya ke bada kuɗin cefane.

Ya ce matarsa ​​da agogolin nasa suna barinshi cikin halin yunwa, duk da cewa shine ke bayar da kuɗin abinci a gidan.

A cewarsa, lamarin ya fusata shi, sai kawai ya zuƙi man fetur ɗinsa daga inji ya zuba a dakin yaran daga bisani ya kunna wuta.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne Ojo ya bankawa ɗakin da agololin sa ke kwana da wuta a gidansa da ke Fagun, a cikin garin Ondo, hedikwatar ƙaramar hukumar Ondo ta Yamma.

Jamu’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ondo Funmi Odunlami, ta bayyana cewa uku daga cikin yaran biyar sun mutu sakamakon raunukan da suka samu bayan da mijin uwarsu ya babbakesu da wuta.

Odunlami ta ƙara da cewa sai da tsohon ya ya kwashe nasa ‘ya’yan waɗanda tagwayene su biyu, ya ware su daga ɗakin ya kai su wani ɗakin na daban kafin ya ya sanya wuta a ɗakin da agolan nasa suke.

Leave a Reply