Yadda mace ta kashe mijinta saboda rashin fahimtar juna

0
309

Wata mata mai suna Perpetual Onyekachi ta daɓa wa mijinta, Okoro Ndukwu wuƙa lamarin da yayi sanadiyar mutuwarsa.

Lamarin ya abku ne a ƙaramar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni ta jihar Ribas.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba a unguwar Okposi Omoku sakamakon rashin fahimtar juna da ya ɓarke a tsakaninsu.

Wata majiya ta yi zargin cewa ma’auratan masoya ne tun suna makarantar sakandare kafin su yi aure.

A cewar wata majiya, ma’auratan sun samu rashin fahimta ne a safiyar ranar Alhamis, kuma abokansu sun yi ƙoƙarin sasantasu.

Wani daga cikin abokan nasu ya bayyana cewa taron sulhun ya ci tura inda Perpetual da mijinta suka sake fafatawa, lamarin da ya sa ta daɓa masa wuƙa a cikinsa.

Majiyar ta ce an garzaya da Okoro asibiti domin yi masa magani, amma ya rasu, daga nan kuma aka miƙa matar ga jami’an ‘yan sanda da ke sashin ‘yan sanda na Omoku.

Leave a Reply