Yadda jana’izar sojojin rundunar da ke kare shugaban ƙasa da aka kashe a Abuja ta kasance

0
488

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta binne sojoji biyar da ke rundunar kare shugaban ƙasa waɗanda ‘yan bindiga suka kashe a kwanakin baya.

An binne sojojin ne a maƙabartar Guards Brigade da ke Maitama , Abuja, a cewar sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Godfrey Anebi Abakpa. Cikin waɗanda aka binne har da Kyaftin Attah Samuel.

Yayinda ake bankwana dasu

“Kafin rasuwarsu, sojojin suna aiki a Bataliya ta 7 da ke barikin Lungi da ke Maitama da Bataliya ta 176 da ke Gwagwalada a birnin tarayya Abuja,” a cewar sanarwar.

Shugaban rundunar Laftanar Kanar Salim Yusuf Hassan ya bayyana Kyaftin din da kuma sauran sojojin a matsayin kwararru a fanninsu kuma sun jajirce wajen kare martabar Najeriya.

A watan jiya ne wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojojin kwanton-bauna a yankin Bwari da ke Abuja inda suka kashe su.

Leave a Reply