Yadda aka yi Salatul Ga’ib ga marigayi Alhaji Aminu Dantata
Daga Jameel Lawan Yakasai
Sallar Ga’ib wacce majalisar malamai ta jihar Kano ta gabatar karkashin shugabanta Malam Ibrahim Khalil. Kafin sallar babban Kwamandan Hisba na Kano Sheikh Mal.Aminu Daurawa ya bayyana dalilan dayasa ake sallar Ga’ib Maigirma Mataimakin Shugaban Majalisar dattijai DSP Barau I.
KU KUMA KARANTA: Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya bar mana wasiyar a binne shi a Madina idan ya rasu – Inji iyalansa
Jibrin shine ya wakilci fadar shugaban kasa wajen sallar. daruruwan mutane daga kano da wasu jihohi dake makwabtaka suka halacci wajen.
alluma da dama sun bayyana marigayin a matsayin uba dattijo wanda yake da hakuri dakuma dauke kai ga duk wani abu dazai kawo rudani, sunyi kira ga gwamnatin tarayya data samar da wani aiki wanda za a saka sunanshi domin kara martabawa.