Yadda ɗalibi ya kashe abokinsa bayan ya daɓa masa wuƙa a Bauchi

1
522

Daga Ahmad SAKA, Bauchi

Jami’an ‘yan sandan jihar Bauchi, sun kama wani matashi mai suna Kamaluddeen Musa mai shekaru 22, ɗalibi a kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa da ke karamar hukumar Kangere-Bauchi bisa laifin kashe abokinsa kuma ɗalibin makarantar sabida saɓani.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi.

Ya ce, “A ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin karfe ɗaya na rana, bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa a ranar da misalin karfe 9:15 na safe, Kamaluddeen Musa ya daba wa abokinsa Usman Umar wuƙa, mai shekaru 25 , a cikinsa”

KU KUMA KARANTA:Yadda amarya ta kashe kishiyarta akan tsire

Wakil ya ce lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin; sun ɗauki wanda aka daɓa wuƙan, zuwa Asibitin ƙwararru na Bauchi, inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu, yayin da nan take aka kama wanda ake zargin.

Ya ce, “Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda ake zargin da wanda aka kashen abokanai ne kuma ɗaliban makarantar sakandare ta Adamu Tafawa Balewa College of Education Kangere, Bauchi LGA, Jihar Bauchi.

“Kuma a ranar 28 ga Nuwamba, 2022 da misalin karfe 09:15, an samu ‘yar hatsaniya a tsakanin su, a lokacin da marigayin ya yi kukan cewa wanda ake zargin ya fita ba tare da sanar da marigayin ba, lamarin da ya haifar da fada wanda ya yi sanadin rauni a yatsar wanda ake zargin, ana cikin haka sai wanda ake zargin ya zaro wata karamar wuka daga aljihunsa ya daɓa wa marigayin, a cikinsa.

KU KALLI BIDIYON ANAN:https://fb.watch/h8EhyaqX_A/

“Shaidun sun tabbatar da hakan; Musa Danjuma mai shekaru 22 da Nawasi Sadi mai shekaru 20, dukkansu daliban makaranta ne da suka shaida lamarin”

Kakakin ‘yan sandan ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kamar dai yadda aka yi a lokacin da aka bada labarin, domin gano ƙarin bayanai bayanan.

1 COMMENT

Leave a Reply