WHO ta koka kan yadda ƙwararru suka kasa gano dalilin ɓarkewar cutar Corona

0
66
WHO ta koka kan yadda ƙwararru suka kasa gano dalilin ɓarkewar cutar Corona

WHO ta koka kan yadda ƙwararru suka kasa gano dalilin ɓarkewar cutar Corona

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar lafiya ta duniya ta ce har yanzu ta gaza cimma burinta na gano ta inda cutar Corona ta faro da kuma dalilin fantsamarta zuwa sassan duniya, kuma har yanzu babu cikakken bayani kan abinda ke hana binciken nata cimma nasara.

KU KUMA KARANTA: Mazauna Kano sun yi ƙira da Gwamnatin tarayya wajen kawo ƙarshen cutar zazzaɓin cizon sauro

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan, yana mai cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa don bankaɗo gaskiyar lamarin, yana mai cewa ko a baya-bayan nan sai da aikin binciken na wasu gungun ƙwararru ya kasa cimma nasara.

Cutar Corona na cikin cutukan da suka fi gigitar da duniya, wadda ba za’a taɓa mantawa da ita a duniya ba, la’akari da yadda ta yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane, da kuma tilasta sanya dokar hana shige da fice matakin da ya tsayar da duniya cak.

Leave a Reply