Wata mata a Jigawa, ta kona kanta, saboda mijinta ya sake ta

0
49
Wata mata ta ƙona kanta, saboda mijinta ya sake ta a Jigawa

Wata mata a Jigawa, ta kona kanta, saboda mijinta ya sake ta

Wata mata ‘yar shekara 40 (an sakaya sunanta) ta cinna wa kanta wuta bayan mijinta ya sake ta a ƙaramar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

DSP Lawan Shiisu, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, PPRO, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a Dutse, a ranar Juma’a.

Shiisu ya ce matar da ke zaune a ƙauyen Garin Mallam ta zuba wa kanta man fetur sannan ta banka wuta.

“A ranar Alhamis da misalin ƙarfe 7:40 na safe, rundunar ta samu labari mai ratsa zuciya da ban tausayi na wani lamari da ya faru a Guri, wanda ya nuna cewa wata mata ƴar shekara 40 a kauyen Garin Mallam ta zuba wa kan ta man fetur ta kuma cinna wuta, inda ta kone kurmus.

KU KUMA KARANTA:Yadda kaka ta cinna wa ɗanta, matar shi da jikokin ta wuta a Ondo

An ruwaito cewa ta aikata kisan kan ne a wajen garin kauyen.

“Bayan wannan rahoton, tawagar jami’an hedikwatar ’yan sanda ta Guri sun yi tururuwa zuwa wurin inda su ka tabbatar da faruwar lamarin.

“Jami’an sun kai konannen jikin zuwa asibiti, daga baya kuma suka mika gawar ga ‘yan uwa domin yi mata jana’iza,” in ji Shiisu.

Ya bayyana cewa binciken farko da aka yi ya nuna cewa marigayiyar ta samu damuwa ne watanni kadan bayan auren ta da mijinta ya mutu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here