Wasu ma’aurata sun biya ladan $1,000 ga wanda ya gano akunsu da ya ɓata

0
420

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Rustoma babban Aku ne wanda ya tsere daga gidansu lokacin da aka bar ƙofa a buɗe.

Ɓacewar Rustoma ta shiga cikin kanun labarai, bayan da masu shi, wasu ƴan jihar Karnataka da ke kudancin Indiya suka sanya tukuicin kuɗi ga duk wanda zai iya dawo da shi.

Lokacin da aka dawo da Rustoma lafiya bayan kwana biyar, danginsa sun yi farin ciki sosai, har ma suka bayar da kyautar rufi 85,000, kwatankwacin naira 600,000, fiye ma da ladan da suka sanya tun da farko.

Lokacin da abokiyar zamansa Rio taga ya dawo gida bayan kwanaki biyar, ta yi farin ciki sosai har ta sumbace shi a baki.

Iyalan Shetty sun ce sun sayi akun biyu ne daga birnin Bangalore shekara uku da suka wuce.

Ba laifi ba ne kiwon aku a Indiya, amma masu ra’ayin kare haƙkin dabbobi na bayar da shawarar hana kiwo da cinikin tsuntsaye masu ban sha’awa a Indiya.

“A ko yaushe muna ɗaukar su a matsayin ɓangare na danginmu kuma ba mu taɓa yarda da saka su a keji ba,” in ji Arjun Shetty, wani ɗan kasuwa.

Tsuntsayen, in ji shi, suna son zama tare da iyalan, musamman Vihan, ɗan Mista Shetty me shekaru bakwai, kuma suna son kwaikwayon sautin da suke ji a kusa da su.

Rio (matar Akun) ta damu matuƙa da ɓacewar abokin zamanta har ta daina cin abinci.

Mista Shetty ya ce ya kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bugawa da rarraba takardu masu ɗauke da hoton Rustoma, da kuma tukwicin da ya kai rufi 50,000.

Sun sanya allunan a kan tituna da dama a cikin garin Tumakuru, inda suke zaune. Iyalin kuma sun biya masu shela a unguwanni don zagayawa suna cigiyar Rustoma da lasifika.

Yayin da wannan ke faruwa, Rustoma bai yi wani nisa da su ba, don bai wuce kilomita uku da inda suke ba, inda ma’aikata biyu, Srinivas da Krishnamurthy ke kula da su.

Krishnamurthy ya samu Rustoma ne kwana guda bayan ya bar gida, inda ya ga tsuntsun zaune a saman bishiya, yana ƙoƙarin kare kansa daga maguna da karnuka, ya dube shi ya ga ya jigata ƙwarai saboda yunwa.

Rustoma ne ya amince ya tafi tare da Krishnamurthy, Bayan kwana huɗu a hannun mutanen sai mariƙansa suka ga cigiyar, nan take suka kira Shetty.

A lokacin ne suka gane cewa ladan ya ma fi abin da aka yi alkawari.

“Mun tuntuɓi wani limamin coci wanda ya ce Rustoma zai dawo nan da kwana uku, amma ya ce mana zai iya faruwa da wuri idan muka ƙara adadin ladan,” in ji Mista Shetty.

Lokacin da ya je karbar Rustoma, akun na zaune a cikin kejinsa, cikin tsananin bacin rai.

“Na so a ce kun ga yadda ya rikice lokacin da ya gan ni, nan da nan ya fara wasu surutai da yake yi duk sa’ad da yake cikin farin ciki da jin dadi”, in ji Mista Shetty, yana ƙyalƙyala dariya.

Duk danginmu sun yi murna da dawowar Rustoma, ba ma kamar Rio, Mista Shetty ya ce za su sanya ido ƙwarai ƙwarai a kan tsuntsayen a yanzu.

Sai dai girgizar da ɓacewar Rustoma ta haifar a danginsu, ta sa mutanen na tunanin ko tsuntsayen za su fi jin dadi a wani yanayi mai girma kamar gidan ajiye namun daji a Indiya ko kuma a waje.

“Shin iyaye ba sa tura ƴaƴansu ƙasashen waje don su yi karatu rayuwarsu ta yi kyau? Ai ba lallai ba ne su zauna tare da mu,” in ji shi.

“Idan za su fi farin ciki a can, a shirye muke mu amince da ra’ayinsu”.

Leave a Reply