Wani mutum ya kulle mayu biyu, yai musu fyaɗe a gidansa

0
500

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Alfred, mai shekara 43 gwauro ne daga ƙasar Saselamani, a wajen Giyani, Afirka ta Kudu. Ya kulle wasu da ake zargin matsafa ne a cikin gidansa, kuma ya yi lalata da su na tsawon sa’o’i.

Maƙwabtansa da suke shirin ƙona matan mayu sun ce: “Babu shakka mun kama su suna yin maita, kuma an ce a ƙone su. A hanyata ta zuwa aiki da misalin karfe 4 na safe, na ga matan nan biyu tsirara makale a cikin farfajiyar Alfred.

“Na kira shi ya fito, kuma ina tara sauran jama’a domin su kawo man fetur da tayoyi don yin abin da ya kamata a yi, se Alfred yace kada ku damu. Zai hukuntasu yadda ya kamata, ya jawo su cikin gidansa, ya kulle ƙofa.”

Makwabcinsa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ya ji kururuwa da ihu na fitowa daga gidan, kuma Alfred ya ƙi buɗe kofar.

“Na yanke shawarar kiran ‘yan sanda, wanda suka iso bayan ‘yan sa’o’i. Ina tsammanin idan ya kashe su duka shi kaɗai, zai je gidan yari saboda kisan kai saɓanin idan hukuncin da al’adar su ta yanke na ƙona masu tare da jama’a. ‘yan sanda suka zo suka harba kofa, kuma naga abu ne da ban taba gani ba. Ya ɗaure su akan teburi, yana abu kamar dabba.”

‘Yan sandan sun kai dukkan su uku zuwa ofishin ’yan sandan yankin, kuma a ranar ne aka sake su. Matan sun ƙi buɗe ƙarar Alfred duk da cewa ya ci zarafinsu fiye da sa’o’i uku.

Alfred ya ce: “Na yi abin da na yi domin na ga sun riga sun yi min sihiri.

“Wani Pasto ya ce min akwai wasu mata guda biyu sunata min sihiri cewa kada in ƙara aure, don haka ina so in huce bacin rai na akansu.”

‘Yan sandan sun ce sun ƙyale Alfred ya tafi bayan su ukun sun yi musafaha tare da yarda ba za su sake damun juna ba.

“Alfred ya gargadi matan biyu da su ce ba za su sake yi masa sihiri ba idan suna so su tsira daga gare shi.”

Leave a Reply