Wani dan Ilorin ya bankawa gidansa wuta ƙurmus don huce takaicin matarsa

1
388

An tabbatar da faruwar lamarin daga bakin me magana da yawun hukumar kashe gobara na jihar kwara, Hakeem Ade kunle, inda yace lamarin ya faru ne da misalin qarfe 10:28 na safiyar Lahadi, a Lekki fes wan, unguwar Eyenkorin a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Yace wani mr Kola dake zaune a unguwar, shine yayi gaggawar kiran hukumar kashe gobarar, domin sanar dasu tashin gobarar.

Jami’in, Ya qara da cewa sun kashe gobarar akan lokaci tare da hanata yin ta’adda ko fantsamawa zuwa wasu gine gine.

Daily post ta rawaito da cewa megidan yafada ”dagangan na watsa wuta a ɗakuna na guda uku, sannan na banka wutar saboda takaicin matata.”

1 COMMENT

Leave a Reply