Wani ɗan asalin Jihar kano, mazaunin Faransa ya ƙirƙiro hanyar auna tsayin bishiya
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Dr. Mubark Mahmud PhD, mai bincike kan muhalli ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya, inda ya ƙirƙiri sabuwar hanyar auna tsawon bishiya wanda duniyar kimiyya ta karba ta kuma raɗa wa binciken suna “Mahmud Method”.
An saka a manhajar M-Tree da jami’o’i a Faransa ke amfani da ita wajen auna tsayi da kauri na bishiyoyi.
Read also:Iyayen yara sun nemi ɗaukin Gwamnatin Kano akan Makarantar Sakandiren Kwakwaci da ta lalace
Tuni dai aka ƙaddamar a jami’ar da ya ke karatu, université Paris-Saclay a ranar 30 ga watan Afrilu.
Tuni dai aka wallafa wannan bincike a wata mujallar noma mai suna Smart Agricultural Technology Kuma za’a saka shi a manhajojin koyarwa a makarantu da cibiyoyi da dama.
Hakazalika an bayyana cewa akwai shirin za a bunƙasa binciken ta hanyar saka shi a ƙirkirarriyar fasaha wato Artificial Intelligence, AI.