Wanda ya ƙirƙiro maganin zubar da ciki ya mutu
Daga Ibraheem El-Tafseer
Farfesa Etienne-Emile Baulieu, wanda ya ƙirƙiri maganin zubar da ciki na RU 486, a ranar 5 ga watan Disamban 1984, birnin ParisAsalin.
Ƙwararren mai binciken kimiyya wanda ya ƙirƙiri maganin zubar da ciki, Étienne-Émile Baulieu ya mutu yana da shekara 98 a duniya.
Dr Baulieu ya ƙirƙiro maganin zubar da cikin ne a shekarar 1984.
Bayan ƙirƙiro shi, maganin mifepristone ya kawo sauyi a tsarin haihuwa a duniya.
READ ALSO: Muna ƙira ga gwamnatin Kano da ta samar mana da Asibiti – Al’ummar Unguwar Magashi
Maganin nasa ya bai wa mata damar kauce wa yin tiyata domin zubar da ciki, da kuma yanke hukunci a kan rayuwarsu.
Maganin nasa ya shiga cikin magunguna masu muhimmanci ga hukumar lafiya ta duniya.
Matar Dr Baulieu ta ce binciken da ya yi sun zamo abubuwan kawo ci gaban rayuwa a duniya.