Usman Abdallah ya ajiye aiƙin Horars da Ƙungiyar Kwallon ƙafa ta Kano Pillars

0
34
Usman Abdallah ya ajiye aiƙin Horars da Ƙungiyar Kwallon ƙafa ta Kano Pillars

Usman Abdallah ya ajiye aiƙin Horars da Ƙungiyar Kwallon ƙafa ta Kano Pillars

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babban mai Horars wa Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars Usman Abdallah, ya sanar da ajje aikin horar da Kano Pillars ne a ranar Laraba data gabata, kamar yadda sashen yada labarai na kungiyar ya sanar.

Sai dai bai bayyana dalilan ajje aikin ba, sai dai kungiyar ta Kano Pillars ta yi mishi fatan alkhairi na tsawon lokacin da ya yi aiki tare da ita.

KU KUMA KARANTA: An dawo da mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Abdallah, bayan dakatar da shi

Sai dai Abdallah ya ce ya yanke shawarar ne sakamakon wata gagarumar dama da ya samu kuma ba zai iya hada aiki biyu a lokaci guda ba matukar yana san cimma nasara.

Leave a Reply