UNICEF ta buƙaci Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin gaggawa na kare makarantu a ƙasar

0
119

Daga Maryam Umar Abdullahi

Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya bayyana buƙatar ƙara ƙaimi wajen inganta batun kiyaye lafiya da tsaron makarantun Najeriya.

Da ta ke bayani yayin bukin ranar ilimi ta bana, wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms. Cristian Munduate tace, a yayin da Najeriya ta nuna aniyar samarda kyakkyawan yanayi a makarantu ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar kare makarantu tare da samarda ƙa’idojin tabbatar da hakan, har yanzu akwai sauran damar ingantawa.

“A wannan muhimmiyar rana, muna sane da hakkin daya rataya a wuyanmu na kare makarantu domin ‘ya’yanmu.” In ji ta.

Munduate ta ƙara da cewar, sau da dama neman ilmi na gamuwa da cikas sakamakon hare-haren da ake kaiwa al’ummomi da makarantu, al’amarin dake kaiwa ga satar ɗalibai.

Waɗannan ƙalubale sun fi tasiri akan ‘yanmata, abinda ke ƙara kassara karatun ‘ya’ya mata a Najeriya.

UNICEF tace hare-haren baya-bayan nan akan makarantu, musamman a shiyoyin arewa maso gabas da yammacin Najeriya, sun kassara karatun fiye da yara milyan 1 da dubu 300, abinda ya sabbaba ɗaukar matakan rigakafin rufe makarantun.

Hakan, in ji UNICEF, ya sake bayyana mahimmancin ɗaukar matakan gaggawa na magance matsalar rashin tsaro a makarantu yadda ya dace.

Asusun na UNICEF ya kuma buƙaci a ɗauki mabambantan matakan inganta tsaron makarantu, duba da ƙwazon da jihohi suka nuna wajen ɗaukar matakan tabbatar da tsaro a makarantu.

Wannan mataki ya kamata ya ƙunshi samarda cikakken tsari da kulawa tare da samarda wadatattun kuɗaɗe, musamman a jihohin dake fama da rashin tsaro.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Chaina za ta taimakawa Najeriya wajen gina tashar wutar lantarki

Munduate ta bayyana aniyar UNICEF na ci gaba da aiki tare da gwamnatin Najeriya da masu bada gudunmawa da ƙungiyoyin bada agaji wajen tabbatar da cewar kowane yaro ya samu ingantaccen ilmi cikin zaman lafiya da tsaro.

Ƙididdigar baya-bayan nan ta nuna cewar, a bisa ƙiyasi, kaso 43 cikin 100 ne kacal na ka’idojin kiyaye makarantu aka cika a kimanin makarantu 6000 da aka nazarta, UNICEF ya tabbatar da samun wannan katafaren ci gaba na baiwa yara milyan 7 da 200, 000 damar samun ilmi a sansanonin ‘yan gudun hijra dake faɗin Najeriya, sakamakon haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu tallafawa da kuma ƙungiyoyin bada agaji.

Wannan bincike ya haska irin ƙalubalen dake akwai wajen kiyaye gine-ginen makarantu tare da takaita hatsarin tashe-tashen hankula da bala’o’i.

Taken ranar ilmi ta bana, “ilmi domin samun dawwamammen zaman lafiya, ya tuna mana irin mahimmancin da ilmi keda shi wajen samun wanzuwar zaman lafiya da daidaito.

“Wannan matashiya ce ga dukkanin masu ruwa da tsaki-da suka haɗa da gwamnatocin tarayya dana jihohi, ƙungiyoyin raya ƙasa dana fafutukar farar hula da al’umma da sauran masana game da muhimmancin samar da makarantu masu cikakken tsaro”, in ji ta.

Leave a Reply