Tsohon Shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonathan, ya nesanta kansa da takara a 2027

0
118
Tsohon Shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonathan, ya nesanta kansa da takara a 2027

Tsohon Shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonathan, ya nesanta kansa da takara a 2027

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya nesanta kansa daga wani sako da aka wallafa a shafin Instagram da ke nuni da cewa yana shirin sake dawowa a zaben shugaban kasa na 2027.

Sakon, wanda wani asusu mai sunan Jonathan ya yada, ya soki shugabannin Najeriya a yanzu, inda ya ce suna “barci”, yayin da ya bukaci ‘yan kasar nan da su zabi shugabanci nagari a 2027.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyoyi a Yobe ta Kudu sun buƙaci Tumsah ya tsaya takarar gwamna a 2027 (Hotuna)

“Tunda shugabannin mu na yanzu suna yin kamar suna barci, muna addu’ar mu dawo da kyakkyawan shugabancin mu a 2027; zabinku shine zai tabbatar da ci gaban makomarmu,” a cewar sakon.

Sakon yana dauke da kade-kade da wani hoto, wanda aka yi imanin cewa AI ce ta samar, na Jonathan yana musabaha da shugaban Amurka Donald Trump.

Sai dai da aka tuntubeshi a ranar Juma’a, Ikechukwu Eze, mai magana da yawun Jonathan, ya yi watsi da sakon a matsayin na karya kuma ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ba ya amfani da shafin Instagram.

“Tsohon shugaban kasa Jonathan bai mallaki asusun Instagram ba,” in ji Eze.

Leave a Reply