Tsohon shugaban ƙasa Umaru ‘Yar’Adua ya cika shekaru 15 da rasuwa
Daga Shafaatu Dauda Kano
A ranar 5 ga watan Mayu, 2025, aka cika shekaru 15 da rasuwar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua, wanda ya rasu a shekarar 2010 yana rike da madafun iko.
An haifi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua a ranar 16 ga watan Agusta, 1951, a garin Katsina. Mahaifinsa, Alhaji Musa Yar Adua, shi ne tsohon Ministan Legas a Jamhuriya ta Ɗaya, kuma yana rike da sarautar Matawallen Katsina, wadda daga baya marigayi Umaru Musa Yar Adua ya gada.
Yar’Adua ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Rafukka a shekarar 1958, sannan aka mayar da shi makarantar kwana ta Dutsinma. Daga nan ya ci gaba da karatu a Kwalejin Gwamnati ta Keffi (1965–1969), sannan ya tafi Barewa College, inda ya kammala a 1971.
Ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1972, inda ya karanta ilimin koyarwa da kimiyyar sinadarai, ya kuma kammala a 1975. Daga bisani, a shekarar 1978, ya sake dawowa jami’ar don yin digiri na biyu a fannin kimiyyar sinadarai.
KU KUMA KARANTA:Taƙaitaccen tarihin Ahmadu Haruna Zago
Aikin farko da ya fara shi ne koyarwa a Holy Trinity College da ke Legas (1975–1976), kafin ya koma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Zaria (1976–1979), sannan daga baya ya koyar a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Zaria har zuwa 1983.
A fagen siyasa, ‘Yar Adua ya fara a jamhuriya ta biyu inda ya kasance dan jam’iyyar PRP, duk da cewa mahaifinsa na daga cikin jagororin jam’iyyar NPN. A lokacin shirin maido da mulki ga farar hula da Janar Ibrahim Babangida ya yi, ya shiga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar People’s Front ƙarƙashin jagorancin ɗan uwansa Janar Shehu Musa Yar Adua, wadda daga baya ta koma jam’iyyar SDP.
A 1991, ya tsaya takarar gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin tutar jam’iyyar SDP, inda ya fadi zabe a hannun Sa’idu Barda na NRC. A 1999, ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, inda ya yi nasara, kuma an sake zaɓensa a 2003.
Umaru Musa ‘Yar Adua ya kafa tarihi a matsayin gwamna da shugaban ƙasa na farko a Najeriya da ya bayyana kadarorinsa na dukiya, mataki wanda da yawa suka yaba da shi a matsayin ƙoƙarin yaki da cin hanci da rashawa.
Allah Ya yi masa rasuwa ranar 5 ga watan Mayu, 2010, yana da shekara 58 a duniya. Ya rasu ya bar mata daya, Hajiya Turai Yar Adua, da ‘ya’ya bakwai, maza biyu da mata biyar.