Tinubu ya amince da sababbin naɗe-naɗe a hukumomin gwamnati guda 7

0
53
Tinubu ya amince da sababbin naɗe-naɗe a hukumomin gwamnati guda 7

Tinubu ya amince da sababbin naɗe-naɗe a hukumomin gwamnati guda 7

Daga Ali Sanni

Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin wasu kwararrun ‘yan Najeriya bakwai da zasu shugabanci wasu hukumomi dake karkashin ma’aikatar jin kai, da kau da bala’o’i da ci gaban al’umma na tarayya.

Waɗanda aka naɗa sun haɗa da:

1 – Badamasi Lawal: Zai kula da hukumar NSIPA, Badamasi Lawal ɗan asalin jihar Katsina ne.

2 – Funmilola Olotu: Za ta kula da ma’aikatar NSSCO.

3 – Aishat Alubankudi: Za ta kula da bangaren kula da mutane masu rauni, a matsayin babbar manaja.

4 – Aderemi Adebowale: Za ta kula da sashen ciyar da ɗalibai abinci a makaratu.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Sakkwato ya karɓe ikon naɗa sarakuna da Hakimai daga hannun sarkin musulmi

5 – Abdullahi Alhassan Imam: Manajan Shirye-Shirye, Ofishin raba Kudi na Ƙasa.

6 – Ayuba Gufwan: Babban Sakatare, Hukumar Kula da Nakasassu ta Ƙasa.

7 – Lami Binta Adamu Bello: Darakta Janar na Hukumar Hana Fatauci da safarar mutane ta ƙasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here