Tinubu ne zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio

0
91
Tinubu ne zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio

Tinubu ne zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasarar lashe zaɓe don yin wa’adi na biyu a 2027, duk da ƙoƙarin ’yan adawa na ƙalubalantarsa.

Yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗa-baki da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) ta shirya a Abuja, Akpabio ya nuna ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulki.

Za mu dawo a 2027, da sunan Yesu, Amin,” in ji shi.
Za mu yi wa jam’iyyarmu da Shugaban Ƙasa addu’a. Wa’adin mulkinsa na biyu ya tabbata.”

KU KUMA KARANTA:Dole a binciki zargin lalata da Natasha ta yiwa Akpabio – Amnesty

Liyafar, wacce gwamnonin APC, ’yan majalisa, da ministoci suka halarta, ta zama gangamin siyasa, inda shugabannin jam’iyyar suka jaddada nasarorin Tinubu.

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce APC za ta ci gaba da mulki: “Yunƙurin ’yan adawa na ƙwace mulki daga hannun Tinubu ba zai yi nasara ba.

“Dole mu yi amfani da ‘wa’azin siyasa’ don nuna ci gaban da muka samu.”

Duk da cewa Tinubu bai sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a karo na biyu ba, shugabannin APC sun fara gangamin mara masa baya ta hanyar taruka da nuna goyon baya, yayin da ’yan adawa ke sukar hakan a matsayin kamfe.

Leave a Reply