Tarihin Rufaida, likita kuma ma’aikaciyar jinya ta farko a duniya

0
222

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Rufaida Al-Islamia (Rufaida Al-Aslamiya ko Rufaydah bint Sa`ad) (Larabci: رفيدة الأسلمية) (an haifeta kimanin shekara ta 620 AD; 2 BH), ta kasance ma’aikaciyar likitanci da jin dadin jama’a ta Musulunci da aka amince da ita a matsayin mace ta farko musulma ma’aikaciyar jinya kuma mace ta farko Likitan fida a Musulunci. An san ta a matsayin ma’aikaciyar jinya ta farko a duniya.

Daga cikin mutanen Madina na farko da suka karɓi Musulunci, an haifi Rufaida Al-Islamia a cikin ƙabilar Baniy Aslam, ta ƙabilar Kazraj a birnin Madina, kuma ta yi suna saboda irin gudunmawar da ta bayar ga sauran matan Ansar da suka tarbi Annabi Muhammad, a lokacin da ya isa Madina.

An tabbatar da Rufaida Al-Islamia a matsayin ma’aikaciyar jinya, mai tausayi kuma mai shiryarwa mai kyau. Da basirarta ta asibiti, ta horar da wasu mata, ciki har da shahararriyar matar Annabi Muhammad, Aisha bint Abubakar, zama ma’aikatan jinya da aiki a fannin kiwon lafiya. Ta kuma yi aiki a matsayin ma’aikacin zamantakewa, Bugu da kari, ta taimaka wa yara mabuƙata da ɗaukar marayu, da taimakon gajiyayyu.

Rufaida Al-Islamia ta aiwatar da dabarun aikinta na asibiti da gogewar likitanta don haɓaka rukunin kula da marasa lafiya na tafi da gidanka, irinsa na farko da aka taɓa samu wanda ya sami damar biyan bukatun likitancin al’umma. Mafi yawan ayyukanta na likitanci sun ƙunshi tsaftacewa da kuma samar da nutsuwa ga marasa lafiya kafin taci gaba da aiwatar da tsagwaron aikin likitancin ta.

A lokacin yaƙi, Rufaida Al-Islamia ta jagoranci gungun ma’aikatan jinya na sa kai waɗanda suka je fagen fama tare da kula da waɗanda suka jikkata. Ta halarci yaƙin Khandaq, Khaibar, da sauransu.

A lokacin zaman lafiya, Rufaida Al-Islamia ta ci gaba da shiga cikin ayyukan jin ƙai, ta hanyar ba da taimako ga musulmin da suke cikin buƙata.

Rufaidah ta horar da gungun mata abokan aikin jinya. Lokacin da rundunar Annabi Muhammad (SAW) ke shirin tafiya yaƙin Khaibar, Rufaidah da ƙungiyar ma’aikatan jinyarta suka tafi wurin annabi Muhammad (SAW), Sai suka neme shi izni , “Ya Manzon Allah, muna son mu fita tare da kai wajen yaƙi da kuma jinyar waɗanda suka jikkata, kuma mu taimaki Musulmi gwargwadon iko”.

Annabi Muhammad (SAW) ya basu izinin tafiya. Masu aikin agajin jinya sun yi kyakkyawan aiki har Annabi Muhammad ya sanya Rufaida cikin wanɗanda aka ba ganima. Rabon ta ya yi daidai da na sojojin da suka yi yaƙi. Hakan ya kasance don girmama aikinta na likitanci da aikin jinya.

Kyautar Lambar yabo ta Rufaidah Al-Islamia a kowace shekara

Kwalejin Royal na Likitanci da ke Ireland, a Jami’ar Bahrain, tana ba wa ɗalibi ɗaya lambar yabo ta Rufaida Al-Islamia a fannin aikin jinya. Kwamitin manyan ma’aikatan lafiya na asibitin su suke tantancewa. Ana ba wa dalibar da tafi kowa fice wajen ba da kulawar jinya.

Leave a Reply