Tarihin rayuwar Aminu Saira, ƙwazonsa da yawan kuɗinsa

0
489

An haifi Aminu Muhammad Ahmad da aka fi sani da Aminu Saira a ranar 20 ga Afrilun shekarar 1979, a garin gwammaja, a jihar Kano,a Nijeriya.

Ɗan fim sannan mai shirya finafinai a masana’artar Kannywood, kana darakta kuma marubucin labarai wanda ake yiwa kallon hamshakin mai kawo sauyi a masana’artar fim.

Ya taso ne a cikin birnin Kano tare da ’yan uwansa guda biyu wadanda dukkansu ‘yan Kannywood ne kuma ya yi karatun firamare da sakandare ne a Kano, ya kuma yi karatun Alqur’ani a kwalejin Aminu kano ta Islamic and legal studies da ke kano a Nigeria.

Aminu Saira ya bar aikinsa na ɗan kasuwa ya shiga masana’antar shirya fina-finan kannywood a shekarar 2006 tare da fim ɗinsa na farko mai suna ‘Musnadi’ da ya fara fitowa a masana’antar.

Ya shahara bayan fitowar fim ɗinsa Jamila da Jamilu a shekarar 2009, ga duhu ga haske a 2010 da Ashabul Kahfi a 2014, wanda ya ba shi lambar yabo da yawa da suka haɗa da daraktan da yafi kyau (Best Director) na shekarar 2014 na ‘Jurors Choice Awards’

Fim ɗin labarina, wanda yanzu shi ne fim ɗin da aka fi kallo a cikin fina finan shi na kannywood. Shi ne daraktan fitaccen fim TV na labarina a shekarar 2020.

Ya kasance mafi shahara gurin shirya fina-finai a dandalin Kannywood. Abokan aikinsa na sha’awar tsarin aikin sa, amincin sa, da kuma basirar sa.

KU KUMA KARANTA:Tarihin Ali Jita da waƙoƙinsa

Bajintar sa ta fito ne bayan ya saki fim din sa na “Jamila da Jamilu” a shekarar 2009, wannan fim ya taimaka masa gurin samun lambar yabo da dama ciki harda darakta mafi inganci na shekarar 2014.

Aminu Saira da yaran shi

Allah ya azirta shi da yara uku, biyu maza ɗaya mace.

Aminu saira ɗaya ne daga cikin hamshakan darakta. Bisa ga binciken mu, kuɗin Aminu Saira ya kai dalar Amurka miliyan biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here