Ta’aziyyar Ɗantata: Jagororin Jam’iyyar APC a Kano sun ƙauracewa tarbar Kashim Shattima

0
112
Ta'aziyyar Ɗantata: Jagororin Jam’iyyar APC a Kano sun ƙauracewa tarbar Kashim Shattima
Gwamnan Kano Abba a lokacin da ya tarbi Kashim Shettima

Ta’aziyyar Ɗantata: Jagororin Jam’iyyar APC a Kano sun ƙauracewa tarbar Kashim Shattima

Daga Shafaatu Dauda Kano 

Shugabanni da jagororin jam’iyyar APC na jihar Kano sun ƙauracewa tarbar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima, inda Jami’an gwamnatin Kano suka mamaye wajen.

Neptune prime ta rawaito mataimakin shugaban ƙasar ya zo jihar Kano ne domin yin ta’aziyyar rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Dantata ga Iyalansa da al’ummar Kano.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta karyata zargin ciwo bashin Dala Miliyan 6.6 da wasu ƴan APC suka yi mata

Bisa al’ada an saba ganin Shugabanni da jagorori da magoya bayan jam’iyyar APC su fito su hadu da Jami’an gwamnatin Kano domin tarbar mataimakin shugaban Kasar .

Hakan tasa al’ummar jihar Kano suka fara tunanin ko dangantaka ce ta yi tsami tsakanin Shugabanni da jagororin jam’iyyar APC na Kano da Kashim Shattima ? .

Wani bincike da Jaridar Neptune prime ta gudanar ya gano cewa kauracewa tarbar mataimakin shugaban Kasar da yan APC Kano suka yi yana da nasaba da abun da ya faru a Gombe tsakanin masoya Kashim Shattima a Arewa maso Gabas da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya lokacin da jam’iyyar APC ta gudanar da taron ta na yankin Arewa maso Gabas an dan Sami hayaniya bayan da Ganduje lokacin Yana shugaban APC na kasa yaki ambatar sunan Kashim Shattima yayi da ya ke tabbatar da baiwa Tinubu Takarar shugaban Kasa a shekarar 2026.

Wannan lamari shi ne ake zargin ya hana yan jam’iyyar APC na jihar Kano zuwa tarbar mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima .

Amma wasu kuma suna ganin hakan yana da nasaba da saukar Ganduje daga shugaban jam’iyyar APC na kasa, wanda ake zargin kamar Kashim din yana da hannu wajen saukar Gandujen.

Don tabbatar da wancan zargi ko akasin hakan Jaridar Neptune prime ta tuntubi Mai magana da yawun jam’iyyar APC na jihar Kano ta Wayar Salula Alhaji Ahmad Aruwa , Amma ba mu sami shi ba.

Mun kuma tura masa sako ta Whatsapp Amma har lokacin hada Wannan rahoto Aruwa bai amsa sakon da muka tura masa ba.

Leave a Reply