Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga uku da ƙwato bindigogi a Kaduna

0
565

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe ƴan bindiga uku a hanyar Sabon Birni da Dogondawa zuwa Kuyelo da Farin Ruwa.

A wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa sojojin sun yi arangama da ƴan bindigan ne a lokacin da sojojin suka fita shawagi a ranar 3 ga watan Satumba.

Bayan musayar wuta, sojojin sun ce sun kashe mutum uku tare da ƙwato AK 47 guda biyu da ƙundun harsashi tara, da wayoyin oba-oba bakwai da waya ƙirar Techno ɗaya da harsasai 120 da janareto ɗaya da kuma babur.

Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ƴan bindiga ke addaba, sai dai jami’an tsaro sun ce suna samun nasara a kansu.Ko a kwanakin baya ma sai da sojojin suka yi ta kai farmaki yankin Chikun na Jihar Kaduna inda suka kashe ƴan bindigan da dama.

Leave a Reply