Shugaban Sri Lanka ya yi murabus ta hanyar wasiƙa bayan ya gudu zuwa Singapore

0
505

Shugaban Ƙasar Sri Lanka da ke gudun hijira, Gotabaya Rajapaksa, ya miƙa takardar yin murabus a ranar Alhamis, biyo bayan zanga-zangar da aka yi kan taɓarɓarewar tattalin arziki.

Kakakin majalisar ya bayyana hakan ne sa’o’i bayan Rajapaksa ya fice daga ƙasar. Sanarwar ta haifar da farin ciki a babban birnin kasuwanci na Colombo inda masu zanga-zangar suka yi dafifi a wajen sakatariyar shugaban kasar, inda suka bijirewa dokar hana fita a faɗin birnin.

Jama’a sun kunna wuta, suna rera taken kuma suna raye-raye cikin farin ciki a wurin zanga-zangar Gota Go Gama, wanda aka sanya wa suna da izgili bayan sunan farko na Rajapaksa. “Duka ‘yan ƙasar zasu yi biki a yau. Babban nasara ce,” in ji Damitha Abeyrathne, wata mai fafutuka.

Read also: https://neptuneprimehausa.com/sri-lanka-masu-zanga-zanga-sun-mamaye-fada-har-sai-shugabanni-sun-sauka/

Ta ƙara da cewa, “Ba mu taba tunanin za mu sami ‘yantar da ƙasar nan daga gare su ba,” in ji ta, yayin da take magana kan dangin Rajapaksa wadanda suka mamaye siyasar ƙasar ta Kudancin Asiya tsawon shekaru ashirin.

Rajapaksa ya miƙa murabus dinsa ta hanyar imel da yammacin ranar Alhamis kuma zai tabbata a hukumance ranar Juma’a, da zarar an tabbatar da takardar bisa doka, in ji kakakin Gwamnatin.

Rajapaksa ya gudu zuwa Maldives a ranar Laraba sannan ya nufi Singapore ranar Alhamis a cikin wani jirgin saman Saudi Arabiya, a cewar wani wanda ya san lamarin.

Wani fasinja a cikin jirgin wanda ya ce a sakaya sunansa, ya shaida wa Reuters cewa wasu gungun jami’an tsaro sun gamu da Rajapaksa kuma an gan shi yana barin yankin VIP na filin jirgin a cikin ayarin motoci baƙeke. Ma’aikatan jirgin da ke cikin jirgin sun shaida wa Reuters Shugaban, sanye da baƙaƙen kaya, ya tashi cikin ajin kasuwanci (Bussiness Class) tare da matarsa, ​​da masu gadin sa biyu, suna bayyana shi a matsayin me shiru shiru” da “son mutane”.

Ma’aikatar harkokin wajen Singapore ta ce Rajapaksa ya shiga ƙasar ne a wata ziyarar sirri kuma bai nemi mafaka ba ko kuma ba shi mafaka.

Matakin da Rajapaksa ya yanke a ranar Laraba na sanya abokinsa na Firayim Minista, Ranil Wickremesinghe, mukaddashin shugaban ƙasar ya haifar da ƙarin zanga-zangar, inda masu zanga-zangar suka mamaye majalisar dokoki da kuma ofishin Firayim Minista da ya yi murabus.

“Muna son Ranil ya koma gida,” in ji Malik Perera, wani direban rickshaw mai shekaru 29 da ya halarci zanga-zangar majalisar, a safiyar ranar Alhamis. “Sun sayar da Ƙasar, muna son mutumin kirki ya karbi mulki, har sai lokacin za mu daina.”

An shafe watanni ana zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki amma ta dauki wani sabon salo a ƙarshen makon da ya gabata lokacin da dubban ɗaruruwan mutane suka mamaye gine-ginen gwamnati a Colombo, inda suka zargi iyalan Rajapaksa da kewayenta kan hauhawar farashin kayayyaki da suka gudu, da karancin kayan masarufi, da kuma cin hanci da rashawa.

Leave a Reply