Shugaban ƙaramar hukumar Katagum ya raba wa al’umma tallafin kayan masarufi
Daga Idris Ibrahim Azare
A ranar Talata, 13/5/2025 shugaban ƙaramar hukumar Katagum, Hon. Yusuf Babayo Zaki ya ƙaddamar da shirin rabon tallafi na kayan Sana’a, noma, mota da kuma babura a al’ummar mazaɓarsa.
Rabon wanda irinsa ya kasance na farko a shugabancin ƙaramar hukumar Katagum, Yusuf ya ba da sabbin babura roba-roba a dukkan Kansiloli 20 da suke a ƙaramar hukumar tare da S.A Community guda ɗaya da kuma ƙarin mutane 6.
Kyautar da ya ayyana a matsayin kyautata wa don sauƙaƙawa zuwa wajen aiki akan lokaci da kuma zirga-zirgar jama’a, sannan ya ba da Kekunan saƙa, injin ban ruwa, injin markaɗe, injin niƙa, injin murza taliya a mata da matasa don dogaro da kansu da kuma wayoyin hanu ga ‘yan Media domin ƙarfafa musu aikinsu.
A ɓangaren kiwon lafiya ya samar da kayayyakin gwaje-gwaje, katifu da gadajen kwantar da marasa lafiya a asibiti, littattafai da abin karatu don taimakon ɗalibai na matakin karatun farko a makarantun firamare na ƙaramar hukumar Katagum.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Bauchi ta bai wa ɗalibai 4 da suka yi bajinta a JAMB kyautar ₦4m
Sannan ya ba da kyautar mota ga shugaban jam’iyar PDP na ƙaramar hukumar Katagum Mercedes-Benz shi ma don kyautata wa tare da rabon tsabar kuɗi a mutane da dama masu ƙananun sana’a domin dogaro dakai.
Har ilau lokacin da ya ke ƙaddamar da shirin ya sanar da ɗaukan ma’aikata a fannoni daban-daban wanda za a rinƙa biyan su a ƙaramar hukumar Katagum.
Taron wanda aka yi a farfajiyar sakateriyar ƙaramar hukumar ya samu halartan mataimakin shugaban jam’iyar PDP na jihar Bauchi, Alh. Falalu Attah, shugaban jam’iyar PDP na ƙaramar hukumar Katagum Hon. Kabiru Halilu, shugabannin ƙananan hukumomin Giade, Darazo, Hakimai da Dagatai na ƙasar Katagum.
Mutanan da suka samu waɗannan kyaututtuka sun nuna farin cikinsu da wannan kaya da aka ba su wanda za su dogara da kansu.