Shugaba Tinubu ya naɗa Isma’il Ahmed shugaban PCNG
Daga Jameel Lawan Yakasai
Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Jumu’a 27 ga Yuni 2025.
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya yaba da ci gaban da aka samu a Kaduna
Sanarwar ta ce Ismaeel Ahmed zai jagoranci shirin PCNGi wanda aka kirkiro domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur, ta hanyar samar da makamashi mai rahusa da tsafta wato iskar gas da aka matse (CNG).
Tuni dai shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Barrister Ismaeel Ahmed a matsayin Shugaban Shirin, a yunkurin da zai yi wajen kawowa shirin na gwamnati ci gaba.