Sheikh Fantami ya karɓi baƙuncin matashi ɗan Kano da ya ƙirƙiri na’urar taimakon makafi

0
30
Sheikh Fantami ya karɓi baƙuncin matashi ɗan Kano da ya ƙirƙiri na'urar taimakon makafi

Sheikh Fantami ya karɓi baƙuncin matashi ɗan Kano da ya ƙirƙiri na’urar taimakon makafi

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Sheikh Fantami Ya Karbi Bakuncin Matashi Dan Asalin Sharada Da Ya Kirkiri Na’urar Taimakon Makafi da Fasahar Binciken Ma’adinai

Wani matashi mai shekaru 19 daga Sharada dake Jihar Kano, Khalifa Aminu, ya kirkiri na’ura mai taimakawa makafi wajen gano shinge ta hanyar kara, domin saukaka musu tafiya.

Khalifa ya kuma kirkiri wata sabuwar na’ura ta fasaha da ke gano ma’adinai da abubuwan da ke karkashin kasa, abin da ke da matukar amfani ga masana’antu da gine-gine.

KU KUMA KARANTA:Ɗaurarru 62 sun kammala karatun sakandire a gidajen gyaran hali na Kano

A ziyararsa tare da mahaifinsa zuwa wajen tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, a Abuja, Farfesan ya yaba da hazakarsa tare da alkawarin tallafa masa da shawarwari wajen bunkasa fasahohinsa.

Pantami ya kuma ja hankalin Khalifa da ya ci gaba da kirkire-kirkire da za su amfani al’umma tare da bunkasa tattalin arziki.

Leave a Reply