Saurayi ya kashe budurwarsa, ya kuma ƙone gawarta, bayan ya yi mata ciki a Bauchi

0
654

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta samu nasarar cafke wani saurayi mai shekara 27 a duniya, Munkaila Ado bisa zargin kashe budurwarsa mai suna Safiya Danladi, ‘yar shekara 13 a duniya da ke kauyen Pali a karamar hukumar Alkaleri a cikin garin Bauchi. 

Bayanai sun nuna cewa kafin safiya ta mutu tana ɗauke da cikin watanni hudu wanda kuma shi saurayin nata ne ya mata.

A sanarwar da kakakin ‘yansadan Bauchi, Ahmed Wakil ya fitar, ya ce Munkaila ya ɗauki Safiya zuwa jihar Gombe domin zubar da cikin da ya mata, amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

Daga baya kuma, Munkaila Ado ya yanke hukuncin kashe ta bayan rashin nasarar zubar da cikin da ya yi wa budurwar tasa.

Sanarwar ta ce, “Wanda ake zargi (Munkaila) ya bayyana da kansa cewa yarinyar da ta bace ɗin budurwarsa ce da take dauke da cikin watanni hudu da sanin mahaifiyarta ya yi ƙoƙarin zubar da cikin, shi kuma mahaifinta Alhaji Danladi Mohammed ba shi da masaniya.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa “Munkaila ya hada baki da mahaifiyar yarinyar ‘yar shekara 13 da wani mai suna Muazu, inda suka dauki yarinyar zuwa Gombe da nufin zubar da cikin.

“Bayan da suka isa Gombe sun samu wata mata mai suna Hajiya Amina Abubakar mai shekara 50 da gidanta dake Jekada Fari da ke bayan asibitin Kwararru na Gombe, inda aka yi wa yarinyar wasu abubuwa da nufin zubar da cikin”.

Bayan rashin nasarar zubar da cikin, sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin da suke hanyar dawowa Bauchi, Munkaila da Muazu suka shake Safiya har ta mutu.

Daga baya kuma suka ƙona gawarta sannan suka binne ta a wani rami.

‘Yansandan sun ƙara da cewa za su gurfanar da waɗanda suka kama a gaban kotu bisa tuhumarsu da kisan kai gami da cin zarafi da keta haddin ƙaramar yarinya.

Leave a Reply