Sarki Aminu Ado, ya naɗa Aminu Ala ‘Ɗan Amanar Kano’
Daga Shafaatu Dauda Kano
Mai martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya baiwa shahararren mawakin Nan Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) Sarautar Dan Amanar Kano.
Hakan na dauke ne cikin wani Sakon Sarkin da Sarkin Dawaki Babba Aminu Babba Danagundi ya fada , yayin bikin bajekolin wakokin Hausa na bikin sallah da aka gudanar a fadar Sarkin dake gidan Sarki na Nasarawa.
KU KUMA KARANTA:Sarkin Kano Sanusi, ya bawa ‘yan kasuwar waya da iftila’in gobara ta shafa tallafin Naira miliyan 10
Mai martaba Sarkin Kano ya umarce ni da na fadawa Aminu Alan Waka cewa ya daga likkafar Sarautar da ya ba shi lokacin ya na matsayin Sarkin Bichi ta Dan Amanar Bichi zuwa Dan Amanar Kano”
Ya ce Sarkin ya ɗauki wannan matsayar ne bayan da ya Sami shawarwari daga manyan mutane a fadin Nigeria , don haka ya ɗauki shawarar kuma ya nada ka a matsayin Dan Amanar Kano.
Aminu Babba Danagundi ya ce za a saka lokacin da ya dace domin yin bikin nada Alan Waka a matsayin Dan Amanar Kano.