Sanata Sani Musa ya musanta yi wa Sanata Kawu Sumaila gyaran turanci a majalisa
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Sen. Mohammed Sani Musa mai wakiltar Neja ta gabas ya musanta cewa ya tashi a majalisa ya yi wa Sanatan Kano ta kudu Kawu Sumaila kaca-kaca kan rashin yin turanci daidai.
Wannan na cikin wata sanarwa da Sanatan ya fitar da safiyar Lahadin nan.
Ya ce, bidiyonsa da ake yaɗawa, bidiyo ne da aka ɗauke shi tun shekara 2023 lokacin da ya ke martanin ga wani da ba a san kowaye ba, wanda ya yi rubutu ya ke zargin majalisar da yin abubuwan da ba su dace ba a kasafin kudi.
KU KUMA KARANTA:APC na daf da karɓar jiga-jigan NNPP ciki har da ‘yan majalisa – Ganduje
Ya ce, ko a wancan lokacin ba abin da ya haɗa abokinsa kuma ɗan uwansa Sen. Kawu Sumaila da wannan alʼamari.
Sanatan ya ce masu son tada rikici da masu yaɗa labaran ƙarya ne kawai ke yaɗa bidiyon da bayani ba na gaskiya ba.
A baya-bayan nan ne dai, a Social Media har ma da wasu kafafen yaɗa labarai na rediyo a Kano, suka yaɗa bidiyon Sen. Sani Musa wanda aka jiyo yana kokawa kan turanci, inda a ka bada bayanin cewa yana korafi ne kan turancin Sen. Kawu Sumaila a gidan Talabijin.