Sanata Lawal ya sake shan kaye a hannun Machina a kotun ɗaukaka ƙara

1
481

Sugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya sha kaye a ƙarar da ya shigar inda yake ƙalubalantar takarar Bashir Machina.

A ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, 2022, kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke zama a Damaturu a jihar Yobe ta zartar.

Kotun ta ce Bashir Machina ne ɗan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa ba Ahmad Lawan ba.

Honourable Justice Monica Dongban-Mansen wacce ta jagoranci kwamitin mutum uku ta yanke hukuncin ne a wata ƙara da Ahmad Lawan ya shigar gaban kotun, Lawan ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta Damaturu ta yanke.

A cikin ɗaukaka ƙarar, ya buƙaci kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana shi a matsayin halastaccen mai riƙe da tutar jam’iyyar APC a zaɓen sanata mai zuwa. Kotun ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta.

1 COMMENT

Leave a Reply