Saƙon Mansurah Isah zuwa Tinubu

0
513

Daga Saleh Inuwa, Kano

Mansurah ga Tinubu; Zan yi maka kamfen da jinina, kyauta, in ka ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, da har yanzu suna hannun masu bindiga.

Bayyanar bidiyon fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane ya tada hankulan ‘yan Najeriya.

A sabon bidiyon da suka saki, an ga yadda suke zane jama’ar da ke hannunsu da sanyin safiya, inda fasinjojin ke ta kuka cike da ban tausayi. Hakan yasa hankulan mutane ya tashi inda ake ta kira ga gwamnati da ta yi gaggawar yin abinda ya dace domin kubutar da jama’ar.

Ba a bar jaruman Kannwood a baya ba, jarumai irinsu Ali Nuhu da Mansurah Isah sun bayyana tashin hankalinsu.

Wallafar Mansurah Isah ta ja hankalin jama’a inda tayi kira ga ɗan takarar shugabancin Ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, da yayi wani abu akai, ita kuma zata masa kamfen.

Ga wasiƙar kamar haka;

“Zuwa ga Bola Ahmed Tinubu:
Wallahi, idan ka taimaka mana aka sako fasinjojin jirgin kasa Abuja Kaduna waɗanda aka sace, wallahi zan zabe ka, iyalaina zasu zaɓe ka, jama’a ta za su zaɓe ka a yankina, duk wani wanda gidauniya ta ta taɓa amfana zai zaɓe ka. Zan yi maka kamfen da Jinina.

“Za ka iya, ka bada kuɗin da suke buƙata ka yi amfani da kuɗin kamfen ɗin ka ka fitar da su, mu kuma zamu yi maka kamfen kyauta, wallafar ta tace.

Leave a Reply