Rundunar ‘yansanda ta ƙasa ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano Sanusi II

0
62
Rundunar 'yansanda ta ƙasa ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano Sanusi II

Rundunar ‘yansanda ta ƙasa ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano Sanusi II

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wannan umarni ya fito ne ta bakin mai magana da yawun ‘yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, bayan shigar wasu masu ruwa da tsaki na ƙasar nan cikin al’amarin.

Sufeto Janar na ‘yansandan ya kuma umurci rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ta karɓi bayanin sarki Muhammad Sanusi a jihar dangane da abin da ya faru.

KU KUMA KARANTA:Bai dace rundunar ‘yansanda ta gayyaci Sarki Sanusi ba – Shugaban Bankin Stanbic IBTC

Egbetokun ya jaddada cewa janye matakin da aka ɗauka tun da farko yana da alaƙa da kudirin rundunar ‘yan sanda na tabbatar da adalci tare da guje wa siyasantar da ayyukan ‘yan sanda ko fassararsu da wata manufa ta daban.

Leave a Reply