Rundunar ‘yansanda a Kano ta gayyaci Sarki Sanusi II kan karya dokar hawan Sallah
Daga Shafa’atu Dauda Kano
Rundunar ‘yansandan Najeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a yayin bikin Sallah karama a Kano.
Idan za a iya tunawa a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani Usman Sagiru, mai shekaru 20, dan unguwar Sharifai, bisa zargin kisan wani dan Vigillante dake cikin tawagar Sarki Sanusi II bayan sallar idi.
Hakazalika rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin wanda hakan ya sa ya gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin ya amsa wasu tambayoyi.
A cewar wata wasika a hukumance da Neptune prime ta gani mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, kuma mai dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye, kwamishinan ‘yan sanda an gayyaci sarki Sanusi ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sandan Nigeria.
KU KUMA KARANTA:Ina neman diyyar mahaifina – Ɗan Mai Tsaron Sarkin Kano Sanusi da aka kashe
Wasikar ta bukaci Sarkin da ya kai kansa hedikwatar rundunar da ke Abuja sashin tattara bayanan sirri a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025, da karfe 10:00 na safe.
Hukumomin tsaro sun bayyana hana hawan sallah, saboda yiwuwar samun tashin hankali.
An dai zargi Sarki Muhammadu Sanusi da yin hawa ranar Sallah da hawan daushe da kuma Hawan Nasarawa inda ya kai ziyara ga gwamnan jihar Kano.