Rundunar ‘Yan Sanda Kano ta kama manyan waɗanda ake zargi da hannu a kisan gillar DPO din Rano, Marigayi CSP Baba Ali
Daga Jameel Lawan Yakasai
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta sake bayyana takaici da alhini bisa kisan gilla da aka yi wa shugaban caji ofis din ‘yan Sanda na Rano, CSP Baba Ali, yayin da yake gudanar da ayyukansa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, yace rundunar ta dage wajen ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aiki. Bayan gudanar da bincike, an kama mutane arba’in da ɗaya (41), ciki har da wadanda ake zargin su ne suka fi taka rawa wajen aikata laifin.
Yace ‘yan sanda na ci gaba da aiki dare da rana domin ganin babu wanda ya tsira daga cikin wadanda suka hada baki ko suka dauki nauyin wannan kisa na rashin imani ga jarumin ma’aikaci.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matashin da ya kona masallata a Kano
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa Rundunar ta kuduri aniyar tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar. Ya jaddada cewa ba za a yi kasa a gwiwa ba har sai an gurfanar da duk masu hannu a wannan lamari a gaban shari’a.
Rundunar na godewa jama’a bisa fahimta, ta’aziyya da goyon bayan da suke bayarwa, tare da bukatar al’umma da su ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da kuma bayar da goyon baya ga ‘yan sanda a yayin gudanar da bincike.
“Zamu ci gaba da hada kai wajen kare al’umma, tare da tabbatar da cewa duk wanda ke kokarin rugujewar wannan aiki, zai fuskanci hukunci.”
“Rundunar ‘Yan Sanda ta girmama marigayi CSP Baba Ali, tare da yabawa jaruntaka da sadaukarwar jami’anmu da ke ci gaba da fuskantar hadari domin kare rayuwar al’umma da tabbatar da tsaro a Jihar Kano.” Acewar Kiyawa