Rundunar sojin sama taci galaba kan Halilu Tubali, ƙasurgumin dan fashin daji a Zamfara

1
815

Hukumomi a Najeriya sun ce sun tarwatsa sansanin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ya addabi sassan jihohin Zamfara da Katsina, tare da gomman yaransa.

Rundunar sojin saman ƙasar ta tabbatar wa BBC cewa an kashe Halilu Tubali da yaransa a wani hari da jirgin yaƙi da dakarunta suka kai a ƙarshen makon jiya.

Majiyoyi sun ce yana ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan fashin daji da suka fi kuɗi, kuma ya ƙware wajen fasa-ƙwaurin makamai.

Hukumomin sun ce sun samu labarin cewa wannan kasurgumin ɗan fashin daji yana gudanar da wani taro ne tare da yaransa masu yawa, ko da yake dama sun dade suna fakonsa, da wuraren da yake mu’amalarsa.

A cewar hukumomin Halilu Tubali babban mai shigo da makamai ne ga ‘yan fashin daji da ke yankin Zamfara da Katsina, baya ga na shi aikin da yake yi a yankin Sububu da bayan Ruwa a karamar hukumar Anka a jihar ta Zamfara.

Ka zalika an tarwatsa wani rumbun ajiyar makaman Tubali a wannan hari, kamar yadda daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin sama air kwamado Edward Gabkwet, ya bayyana mani.

Sai dai bayanan da na tattaro daga yankin na Muradun sun nuna cewa akai-akai ‘yan bindigar ke yin taruka domin tsara yadda za su rika kai hari kan al’umma ko kuma jami’na tsaro.

Duk da dai babu wani cikakken adadin mutanen da aka kasha ko aka jikkata, amma ta tabbata an lalata sansanin Halilu Tubali wanda hakan a cewar rundunar sojin saman ka iya samar da kwanciyar hankali a yankin na Zamfara da Katsina ganin mummunan tasirin da yake da shi ya yankin.

1 COMMENT

Leave a Reply