Rundunar Ƴan Sandan Jihar Jigawa sun kama mutane 14, tare da ƙwato muggan makamai da kuɗaɗen Jabu

0
117
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Jigawa sun kama mutane 14, tare da ƙwato muggan makamai da kuɗaɗen Jabu

Rundunar Ƴan Sandan Jihar Jigawa sun kama mutane 14, tare da ƙwato muggan makamai da kuɗaɗen Jabu

Daga Shafaatu Dauda Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana wata nasara da ta samu a yaki da miyagun laifuka, inda hadin gwiwar jami’an tsaro suka kai farmaki wani maboyar masu laifi a kauyen Digawa da ke karamar hukumar Birnin Kudu, inda aka cafke mutane 14 tare da kwato kayayyakin da ake zargi da amfani da su wajen aikata laifi.

A ranar 11 ga Yuni, 2025, rundunar ta bayyana wani hari da wasu masu damfara daga kauyen Digawa suka kai kauyen Dumus, wanda ya yi sanadin mutuwar Isma’il Ibrahim mai shekara 60 da jikkatar wasu takwas.

A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Alhamis, an gudanar da wannan samamen ne a ranar 12 ga Yuni, 2025 – ranar dimokuradiyya – inda aka cafke mutum 14 dukkansu maza tare da kwato kayayyakin da ke da alaƙa da laifuka.

Sanarwar ta bayyana cewa samamen ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri ne dangane da wata kungiyar masu damfara da aikata sauran laifuka a yankin.

SP Adam ya ce wadanda ake zargin suna hannun jami’an tsaro yanzu haka domin gudanar da bincike mai zurfi, kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Ya ce, “Wannan samame yana nuna jajircewar rundunar wajen kare al’umma da kawar da masu aikata laifuka daga cikin jama’a. Wannan mataki ya biyo bayan harin da aka kai a kauyen Dumus wanda ya yi sanadin mutuwa da raunata mutane takwas.”

KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a jihar Yobe sun kama wata mata da kashe mijinta da wuƙa

“An kai gawar mamacin da kuma waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Tarayya na Birnin Kudu domin bincike da kuma jinya,” in ji shi.

Daga cikin abubuwan da aka kwato a wajen samamen akwai: “Bindigu tara da aka kera da hannu, bindigu na gargajiya guda 27, manyan bindigu guda 37, babura guda hudu, da kuma kudi na jabu dala guda 12.”

Sauran kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da: “Takardun kudin Kasar Afirka ta Tsakiya guda 188 da ake zargin jabu ne, baka da kibiya, ƙarafa, fatar dabbobi, fayil, awarwaro, na’urar yanka ƙarfe (vice), blower da wasu kayan tsafi na gargajiya.”

Adam ya kara da cewa, bayan kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu domin fuskantar hukunci.

Daga ƙarshe, rundunar ‘yan sanda ta bukaci al’umma da su ci gaba da bada hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani motsi ko ayyuka da ake zargin na laifi ne ga hukumomi, inda ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da an hukunta masu laifi.

Leave a Reply