Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 2 a Benuwai

0
149

Wani sabon rikicin ƙabilanci tsakanin ƙabilar Jukun da Tibi ya yi ajalin mutum biyu, ya kuma janyo asarar dukiya mai tarin yawa a Jihar Benuwai.

Jama’ar yankin North Bank, Unguwar da ke makwabtaka da Makurdi, baban birnin jihar sun tsinci kansu cikin tashin hankali tun ranar Lahadi har zuwa Litinin ɗin da ta gabata.

Kwamandan wata ƙungiyar ‘yan banga ta Operation Shara a yankin North Bank, Nura Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A zantawarsa da Aminiya, Nura Umar ya bayyana cewa rikicin ya yi ajalin waɗansu mutum biyu da ba su ji ba ba su gani ba.

“Gaskiya abin ya yi muni. An ƙona gidaje da dama a unguwar Agatashi da ke kusa da tsohuwar gada, daura da ’yan katako, bangaren mahauta. Faɗan ya samo asali ne a tsakanin Jukun da ’yan kabilar Tibi.”

KU KUMA KARANTA: An kashe gomman mutane a rikicin manoma da makiyaya a Chadi

Ya ƙara da cewa “waɗanda rikicin ya yi ajalinsu  wasu mutane biyu da ke talla a baro. Mun jana’izarsu ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce “masu rikicin sun harbi mutane a cikin coci, amma ba su mutu ba; suna asibiti.”

Aminiya ta tuntubi jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda  a Benuwe, Sufritanda Catherine Anene, amma har kawo lokacin haɗa wannan rahoto ba ta amsa ƙiran da aka yi mata ta wayar tarho ba.

Leave a Reply