Rikici ya ɓarke tsakanin Fulani da al’ummar Gomo a Karim Lamiɗon jihar Taraba

0
109
Rikici ya ɓarke tsakanin Fulani da al'ummar Gomo a Karim Lamiɗon jihar Taraba

Rikici ya ɓarke tsakanin Fulani da al’ummar Gomo a Karim Lamiɗon jihar Taraba

Rikicin ƙabilanci tsakanin Fulani da ƙabilun Gomon ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa a ƙaramar hukumar Karim Lamiɗo a jihar Taraba.

Muƙaddashiyar kakakin rundunar ‘yansandan jihar Taraba, SDP Gambo Kwasha, ta tabbatar da faruwa rikicin da kuma asarar dukiyoyin masu yawa a yankin na Gomon da ke ƙaramar hukumar na Karim Lamiɗo.

Wani matashi wanda lamarin ya faru a idonsa ya shaidawa wakilinmu Lado Salisu cewa, rikicin ya fara ne sakamakon shiga gona da kuma barnar da shanun wani bafulatani suka yi, faruwar wannan lamari ne kuma ya sa mai gona ya fusata har lamarin ya kai ga kashe-kashe wanda ya zuwa yanzu ba a tantance adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.

KU KUMA KARANTA:Fulani sun koka akan yadda ake cin mutuncinsu a shafukan sada zumunta

Ardo Jarenga Galdu, shugaban kungiyar Fulani ta Tapital Pulako Jonde Jam na kasa a tarayyar Najeriya, na daya daga cikin wadanda rikicin ya shafa.

Shi kuma Malan Usman Yakubu, da ke zaman shugaban kungiyar matasa kabilan Gomun, ya ce ba su ji dadin faruwar wannan lamarin ba kasancewar akwai kykkyawar fahimta tsakanin al’ummar Gomon da kabilar Fulani wanda ya kai ga kulla dangantakar auratayya tsakanin kabulun biyu.

A dalilin haka ya yi kira ga matasa daga duk bangarorin kabilan biyu da su yi hakuri kuma su guji daukar doka a hannunsu.

Leave a Reply