RASHIN TSARO: Gwamnatin Jigawa ta rufe makarantu, tare da dakatar da zana jarabawa a jihar

0
255

Gwamnatin jihar Jigawa ta bada umarnin gaggauta rufe makarantu a jihar, hakan ya samo asali ne saboda taɓarɓarewar tsaro.

An rufe makarantun ne a ranar Laraba yayin da dalibai ke kan rubuta jarabawa a makarantun jihar.

Rufe makarantu ya haifar da tashin hankali da damuwa, yayin da dalibai sukai dafifi suna jira a zo a kwashe su zuwa garuruwan su na asali.

Da yake zantawa da manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta jihar Wasilu Umar ya tabbatar da haka saidai bai yi karin haske kan lamarin ba.

Wani shugaban makarantar firamare a daya daga cikin makarantun da ke Dutse, babban birnin jihar, ya ce, “an bukaci mu rufe makarantu, mu kuma tura dalibai gidajen su cikin gaggawa”. Rohotan Neptune Prime.

Kazalika, wani hedimasta ya bayyana cewar, an bada umarnin rufe makarantun ne, saboda tsananta kai hare-hare a yankunan jihar.

Har ila yau, cikin daliban makarantar sakandare ta gwamnatin Nuhu Sunusi, ya shaida wa manema labarai cewa an bukaci kowa ya tafi gidansu ne ba tare da sun zana jarabawar da za su yi gobe ba.

Saidai an dora alhakin rufe makarantun da wani sabon hari da aka kai wa jami’an shige da fice a makon jiya Talata inda aka kashe jami’in guda daya tare da raunata wasu biyu a karamar hukumar Magari da ke jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Adam, ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ba ta bayar da umarnin rufe makarantun ba, kuma ma’aikatar ilimi ba ta yi wa hukumar bayanin abin da ya kai ga yanke wannan shawarar ba zato ba tsammani ba.

Leave a Reply