Ranar ma’aikata, rana ce ta baƙin ciki a gare mu – Ma’aikatan Ruwa a Kano
Daga Shafaatu Dauda Kano
Yayin da ake murnar ranar Ma’aikata ta Duniya a yau 1 ga watan Mayu, ƙungiyar ma’aikatan hukumar samar da ruwan Sha ta jihar Kano, ta ce mambobin ta sun kasance cikin baƙin ciki a yau, duk da cewar rana ce ta farin ciki ga ma’aikata, bisa yadda aka gaza fara biyan su sabon albashi na Naira 71,000 a jihar.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan hukumar samar da ruwan Sha a Kano Kwamared Najib Abdulsalam, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Wakiliyar Neptune prime Hausa a yau Alhamis 1 ga watan Mayun 2025.
“Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha a Kano muna cikin ƙuncin Rayuwa; Muna kira ga gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, kan a sanya mu a cikin sabon tsarin albashin ko ma samu farin ciki kamar sauran ma’aikata, “in ji shi”.
KU KUMA KARANTA:Gwamnan Yobe ya ziyarci aikin magudanar ruwa a Damaturu
A cewar Ƙwamared Najib, duk da ƙorafe-ƙorafen da suka yi a baya kan gaza sanya su a cikin sabon tsarin mafi ƙarancin albashi, amma har yanzu shiru suke je, kusan watanni shida ke nan ba’a fara basu albashin 71,000 ɗin ba.
“Muna zargin cewar, waɗanda suke bai wa gwamnan Kano shawara na ɓangaren shafukan sada zumunta, ba su fiya faɗawa gwamna gaskiya abinda yake faruwa a hukumar samar da ruwan sha ta Kano ba, ya sa har yanzu ba’a biya mana buƙatar mu ba, “in ji Najib”.
Idan dai ba a manta ba, Ma’aikatan hukumar samar da ruwan Sha, sun ɗauki tsawon wasu lokuta suna kokawa kan rashin samun sabon tsarin Albashi, da sauran ƙorafe-ƙorafe, ko da dai tuni hukumar ta ce ana ƙoƙari akan lamarin.