Ranar Ma’aikata: NLC Ta Buƙaci Ma’aikata Da Shiga Harkokin Siyasa Dumu-Dumu A Dama Da Su

0
504

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR kwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kaduna ta yi kira ga ma’aikata da su shiga cikin harkokin siyasa na bangaranci da wanda ba na bangarancin don tallafa wa ‘yan siyasar da za su kare muradun su.

Shugaban Kungiyar na jiha, Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na ranar Mayu a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.

Ya jaddada cewa NLC reshen jihar Kaduna za ta tallafa wa ’yan siyasa ne kawai da za su tabbatar da biyan bukatunsu da muradun dana daukacin al’ummar Jihar.

Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya kuma koka kan yadda malaman makarantun firamare da ma’aikatan kiwon lafiya na matakin farko basa samun albashin su tare da ma’aikatan kananan hukumomi wadanda a mafi yawan lokuta sai a karshen watannin da suka gabata suke karbar albashi wanda a cewar sa ba za a amince da shi ba.

Ya kuma nuna damuwarsa da halin da ‘yan fansho ke ciki a jihar musamman yadda ake jinkirin biyan su alawus-alawus na fansho da tsawaita tantancewa da tsawaita wahalhalun da ba su dace ba.

Shugaban ya yabawa jihar Kaduna bisa gagarumin ci gaba na cigaban ababen more rayuwa musamman a Kaduna, Kafanchan da Zariya duk da haka ya ce shugabanci nagari ya wuce samar da ababen more rayuwa kadai amma ya fi bukatar a hada kai da ‘yan kasa a fannin gudanar da mulki, tabbatar da adalci a cikin al’umma, lura sosai da bin doka da oda da daidaito kana da samar da tsaro.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta canza tsohon salon adawarta a dangantakar masana’antu tare da rungumar sabuwar tsarin duniya na bangaranci da tattaunawa kan al’amuran da suka shafi ‘yancin ma’aikata.

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da wakilin shugaban ma’aikata Kwamared Shehu Muhammad, Dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Kwamared Shehu Sani, Tsohon shugaban Kungiyar ta NLC Kaduna Kwamared Jonathan Musa.

Leave a Reply