Nijar ta dakatar da fitar da dabbobi zuwa ƙetare a gabanin sallah

0
46
Nijar ta dakatar da fitar da dabbobi zuwa ƙetare a gabanin sallah

Nijar ta dakatar da fitar da dabbobi zuwa ƙetare a gabanin sallah

Daga Shafaatu Dauda Kano

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dakatar da fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje domin dakile hauhawar farashi a kasuwannin cikin gida gabanin Sallar Layya.

Ma’aikatar Kasuwanci ta ƙasar ce ta sanar da hakan, tana mai cewa matakin zai taimaka wajen ganin an samu isassun dabbobi a kasuwa lokacin bukin Sallah Eid al-Adha da ake sa ran gudanarwa a farkon watan Yuni

Ministan Kasuwanci, Abdoulaye Seydou, ya ce an hana fitar da shanu, tumaki, awaki da rakuma zuwa waje, musamman zuwa ƙasashe makwabta irin su Najeriya da Cote d’Ivoire.

Ya ce jami’an tsaro sun samu umarnin sa ido tare da ɗaukar mataki kan duk wanda ya karya wannan doka.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Lawal ya gana da ministan bunƙasa kiwon dabbobi

Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyoyin masu tada ƙayar baya a Nijar da yankin Sahel suna amfani da satar dabbobi a matsayin hanya ta samun kuɗin shiga.

Wasu daga cikin dabbobin suna sayar da su a cikin gida, wasu kuma ana fitar da su waje domin taimakawa ayyukansu.

Lamarin satar dabbobi ya sa makiyaya da dama suka bar kauyukansu, lamarin da ke haddasa ƙarancin dabbobi a kasuwa da kuma ƙaruwa a farashi.

Nijar na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke yawan fitar da dabbobi zuwa kasashen waje, kuma sama da kashi 90 cikin 100 na al’ummarta Musulmai ne da ke gudanar da layya a lokacin Sallah.

Leave a Reply