NHRC Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Fatima Da ‘Ya’Yanta 4, Ta Buƙaci ‘Yan Sanda Da Kama Masu Laifin

0
501

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

HUKUMAR kare hakkin bil’adama ta kasa, (NHRC) ta yi Allah wadai da kashe wata mata mai juna biyu mai suna Fatima da ‘ya’yanta hudu haka siddan a jihar Anambra da ake zargin ‘yan kungiyar tsaro ESN ko dai wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba su ka aikata wannan aika-aika.

Bayanin hakan ya zo ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar Daraktan hulda da jama’a ta (NHRC) Fatima Agwai Mohammed, inda ta bayyana cewa, babban sakataren hukumar, Cif Tony Ojukwu SAN ya bayyana kisan a matsayin daya daga cikin munanan laifuka na take hakkin bil’adama da aka taba aikatawa wanda ba lallai ba ne ya siffanta Najeriya a cikin wani yanayi mai matukar muni dangane da harkokin.

Sakataren zartarwa wanda ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake mayar da martani kan kisan da aka yi wa matar da ‘ya’yanta wanda yake marar dadin ji da gani, ya bayyana cewa kasar nan ta dade tana cike da munanan labarai na kashe-kashe, garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, fyade, da dai sauransu.

Mista Ojukwu ya kuma kara da cewa, kashe-kashen da ake yi a matsayin babban cin zarafi ne na ’yancin rayuwa da mutuncin dan Adam, wanda kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya lamunce da Yarjejeniya ta Afirka kan ’Yancin Bil Adama da Jama’a da sauran ‘yan Adam na yanki da na duniya baki daya.

“Wadannan kashe-kashen na rashin hankali ba abu ne da za a amince da su ba, kuma mu a matsayinmu na hukuma muna Allah wadai da shi, muna kuma rokon ‘yan kasa su hada kai da jami’an tsaro, ta hanyar samar musu da muhimman bayanan da za su taimaka wajen zakulo wadanda ke aikata wadannan munanan ayyuka da ta’addanci da kuma tabbatar da an gurfanar da su a gaban kuliya, kuma za a iya hukunta su kamar yadda doka ta tanada,” Ojukwu ya bayyana.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaron ‘yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike mai zurfi kan kisan da aka yi wa Fatima da ‘ya’yanta 4 da nufin yin adalci ga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

“Muna sa ido sosai kan binciken da ‘yan sanda ke yi a wannan harka domin tabbatar da cewa an gaggauta gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata wannan ta’asa ta rashin tausayi tare da hukunta su bisa ga dokokin kasa, yanki da na kasa da kasa.

Babban jami’in kare hakkin bil’adama ya nemi jami’an tsaro musamman ‘yan sanda da DSS da su yi amfani da dabarunsu tare da tura jami’an tsaro karkashin leken asiri domin gano tushen wannan kashe-kashe nan take da kuma sauran kashe-kashe da dama, irin na su Deborah Samuel da sauransu.

Sakataren hukumar ta (NHRC) ya yi amfani da wannan dama wajen nasiha ga ‘yan kasa kan duk wani nau’i na kabilanci ko addini da kuma rarrabuwar kauna da a yi watsi da shi tare da bayyana cewa makiyan dunkulewa ne da hadin kan kasa da ci gaban kasa ke rura irin wannan wutar nuna kiyayya, yana mai tuna cewa Najeriya ta yi nadamar yakin basasa wanda ya zo da asara mara misaltuwa. acewarsa, ta fuskar albarkatun dan Adam da abin duniya, “don haka dole ne mu hada baki mu ce ba za a yi tashin hankali ba don dorewar hadin kanmu a matsayin kasa daya dunkulliya. “

Hakazalika, Babban Lauyan ya gargadi masu fafutuka daban-daban na akida da siyasa, da su rika sanya tsaron Najeriya a gaba fiye da ko wanne irin lamari, yana mai cewa “dole ne mu fara rayuwa cikin lumana a matsayinmu na ‘yan kasa kafin mu tayar da zaune tsaye, kuma a kullum mu kiyaye cewa dora kasar nan kan turbar tashe-tashen hankula da rashin hadin kai zai fi damun mu ko kuma dagula mana matsalolin”.

Ya kuma jajantawa ‘yan uwan ​​wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma bukaci jama’ar yankin da su kwantar da hankulan su, kada su dauki doka a hannunsu, tare da ganin cewa za a yi adalci a karshe.

Leave a Reply