Nana Khadija daga Najeriya ta lashe kujerar kansila a ƙasar Canada

1
821

An bayyana ƴar Najeriya mai suna Nana Khadija Mamudu Haliru, a matsayin ƴar takarar da ta lashe zaɓen kujerar kansila a ƙasar Canada ranar Talata.

Shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya da ke ƙasashen waje, Abike Dabiri-erewa ce ta bayyana haka a kafar Twitter a ranar Laraba.

Ta ce “Ɗaya daga cikinmu ta cimma gaci. Ƴar ƙasar nan a ƙetare mai suna, Nana Khadija Mamudu Haliru ta sanya mu alfahari. Ta tsaya takarar kansila a Ingersoll da ke yankin Ontario a can ƙasar Canada kuma ta lashe zaɓen… Muna taya ta murna. #Ina’alfaharidazamanaƴarNajeriya”.

Zaɓaɓɓiyar kansilar ta garin Ingersoll, Nana Khadija, ta bayyana godiyarta ga mutanen garin da suka aminta da dacewarta kuma suka zaɓe ta. Sannan ta yi alƙawarin za ta jajirce tare da sadaukar da kanta wajen yi masu abin da ya kamata.

Ta ce, “Barkanku, sannan a wannan dare ina taya murna ga dukkanin waɗanda suka lashe zaɓe. Kuma ina godiya ga ba ni dama da kuka yi don na wakilci wannan gari na Ingersoll, sannan zan yi duk mai yiwuwa har cikin zuci tare da sadaukarwa da mai da hankali ga yi muku aiki da ya kamata.””Yanzu mun sami murya, mun yi aiki, kuma mun kai ga gaci, na gode.”

1 COMMENT

Leave a Reply