Nan da 2050 ba za a sake yin aiƙin Hajji cikin tsananin zafi ba – NCM

0
51
Nan da 2050 ba za a sake yin aiƙin Hajji cikin tsananin zafi ba - NCM

Nan da 2050 ba za a sake yin aiƙin Hajji cikin tsananin zafi ba – NCM

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hussein Al Qahtani, mai magana da yawun Cibiyar Kula da Yanayi ta Ƙasar Saudiya (NCM), ya bayyana cewa Hajjin bana zai kasance na ƙarshe da za a yi shi a cikin zafi na lokacin bazara.

Ya ce daga 2026, aikin Hajji zai fara komawa cikin lokutan da yanayin su ya fi sauƙi — kamar lokacin iska lokacin sanyi , da lokacin damina — waɗanda za su bayar da yanayi mai daɗi ga miliyoyin masu ibada a kowace shekara.

Mai magana da yawun ya bayyana cewa nan guda takwas masu zuwa hajji Masu zuwa za su faru a lokacin bazara, sannan hajjoji guda takwas masu biyo baya a lokacin sanyi, kafin su shiga lokacin damina inda zafin rana zai fara ƙaruwa a hankali, kafin a koma lokacin bazara (zafi) bayan kusan shekaru 25.

KU KUMA KARANTA: Saudiyya ta hana Sheikh Gumi shiga ƙasar domin aikin Hajji

Al Qahtani ya ce wannan canji yana faruwa ne saboda juyin da kalandar Musulunci ta wata (Hijri) ke yi, wanda ke baiwa masu niyyar Hajji damar gudanar da ibada a yanayi mafi sauƙi a shekaru masu zuwa.

NCM ta fitar da kalandar Hajji na tsawon shekaru 25 da ke bayyana yadda ranakun Hajji — bisa ga kalandar Hijri — za su yi daidaito da lokutan shekara na kalandar Gregorian har zuwa shekara ta 2050.

Saboda yanayin kalandar Hijri wanda ke da kusan kwanaki 11 kasa da na kalandar Gregorian, ana samun canji na lokacin Hajji zuwa gaba da kusan sati daya a kowace shekara.

Ya ce masu gudanar da Hajji ba za su sake fuskantar zafin rana mai tsanani ba har sai bayan shekaru 25 masu zuwa.

Al Qahtani ya ƙara da cewa za a samu yanayi mai daɗi sosai ga mahajjata har sai Hajji ya dawo cikin lokacin zafi a shekara ta 2050.

Leave a Reply